Ambaliyar ruwan sama da aka shafe kwanaki ana tafkawa ta lalata gadar garin Katarko dake karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Dr Mohammad Goje, Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu ranar Talata.
Ya ce lamarin da ya faru da sanyin safiyar Talata, wanda kuma ya katse kananan hukumomin Gujba da Gulani daga Damaturu babban birnin jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Mutane Da Dama Sun Makale, Yayin Da Gini Ya Rufta A Kasuwar Kano
Goje ya ce ambaliyar ta kuma shafi al’ummar Mutai da Buni Yadi, inda ta lalata gine-ginen gidaje da filayen noma.
Sakataren ya ce hukumar ta tuntubi sojojin da su kafa shingaye a garin Katarko domin hana daruruwan mutane yin tururuwar zuwa wurin.
“An dauki Matakin ne don dakile duk wani hasarar rayuka daga bala’in da ya faru a kan titin daya tilo da ta hada jihar da sauran sassan kasar nan,” in ji shi.
Goje ya ce gwamnatin jihar na samar da wasu hanyoyin da za a sake hada cudanya tsakanin al’ummomin da lamarin ya shafa sakamakon ambaliyar ruwan .
Ya kara da cewa, hukumar ta kaddamar da kungiyoyin tantancewa domin tantance yawan barnar da bala’in ambaliyar ruwa ya haddasa a fadin jihar.
Da yake jajanta wa wadanda abin ya shafa, Goje ya bukaci al’ummomin da su tashi daga gabar kogin zuwa tudu domin gujewa asarar rayuka.
(NAN)
A WANI LABARIN KUMA: Sojojin Najeriya Na Samun Nasarar Murkushe Yan bindiga, Yan ta’adda, Da Masu Garkuwa – Lai Mohammed
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa rundunar sojin Najeriya ta samu nasarori wajen kawar da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a kasar nan. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Mohammed ya bayyana haka ne yayin da ya bukaci masu yan jarida da su kara kaimi bisa fifikon amfanin kasa wajen gudanar da ayyukansu kamar yadda kundun tsarin mulki ya basu.