Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 37 tare da nutsar da gonaki 89,000 a Adamawa
Ambaliyar ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya a fadin jihar Adamawa a wannan damina ta yi sanadiyar mutuwar mutane 37.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa (ADSEMA) wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce wasu mutane 58 sun samu raunuka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Magoya bayan Obi Sun Kalubalanci Yan Sandan Jihar Legas
Hukumar ta ce baki dayan mutane 171,000 ne abin ya shafa, yayin da kadada 89,000 na gonaki suka nutse.
Babban Sakataren na ADSEMA, Dr. Muhammad Suleiman, wanda ya bayyana hakan, ya ce ambaliyar ta yi barna musamman a kananan hukumomin Madagali, Fufore, Yola ta Kudu, Yola ta Arewa, Girei, Demsa, Numan, Lamurde, Guyuk da Shelleng.
Shugaban ADSEMA ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a karshen mako cewa gidaje da sauran gine-gine, kamar makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya, kasuwanni, da gidajen ibada ne abin ya shafa.
Suleiman ya ce ambaliyar ta zarce fiye da yadda ake tsammani ko hasashe, domin bisa hasashen cewa kananan hukumomin da ke gaba da gabar kogin Benue za su shafa, ambaliya ta kai wasu sassan jihar.
“Misali, Madagali, wadda ba a yi tsammanin za ta fuskanci ambaliya ba, bala’in ya afkawa fiye da yadda kananan hukumomin da aka yi hasashe,” in ji shi, yana mai bayanin cewa Madagali bai taba samun ruwan sama mai yawa da ambaliya ba a tarihin baya-bayan nan.
Ya ce Madagali ta rasa mutane biyar daga cikin jimillar mutane 37, sannan wasu shida daga Madagali na kwance a asibiti.
Ya kuma tabbatar da cewa an bayar da taimako ga mabukata, inda ya bayyana cewar bisa ga umarnin Gwamna Ahmadu Fintiri, hukumar ta samar da abinci da kayan abinci a dukkan sansanoni 10 da aka kafa na ‘yan gudun hijira.
A wani labarin kuma: Yan bindiga Sun Sace Basaraken Gargajiya, Matarsa, Da Direbansa
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da basaraken Owa-Onire a gundumar Kwara ta Kudu dake jihar Kwara.
DAILY POST ta samu labarin cewa an yi garkuwa da shi tare da matarsa da direban sa.
Comments 1