Ruwan sama kamar da bakin kwarya, dauke da matsanan cin iska, wanda ya kwashe akalla awanni uku ya na sauka a safiyar jiya Alhamis, ya lalata gidaje a rukunin gidaje na Kundila da ke kallon asibitin horaswa na Aminu Kano da ke kan Zaria road a jihar Kano.
Bayaga wannan wasu gidajen ma dake cikin birnin Kano sun lalace sanadiyar saukan ruwan saman, Wadanda kudaden su ya kai akalla naira milliyan Sittin.
Rukunin gidajen Kundila na kusa da hanyar ruwa ne wanda taso daga gidan gwamnatin jihar Kano, Tarauni da kuma Hotoro da ya hade da dukkannin bangarorin yankin na Zaria Road.
A cewar wani mazaunin yankin da lamarin ya shafa Mai suna Mustapha Haruna ya ce, ruwan samar ya bar al’uma yankin cikin jimami, musamman ma wadanda gidajen su, su ka rushe baki daya.ya yin da wasu su ka tsira da Talbijin, Gado, da kuwa wasu kananan abubuwa, daga cikin gidajen su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Goodluck ya sake samun babban Mukami a Africa
Mustapha ya kuma yi kira ga hukumomi da su kawo musu dauki da kayan agaji.
Sai dai duk yunkurin da a ka yi na tuntubar Kwamishinan Muhalli jihar ta Kano Kabiru Getso, abun ya citira, Amma jami’in Hulda da jama’a na Ma’aikatar Sanusi Na’isa ya ce, ma’aikatar ta san da afkuwar wannan iftila’i.