Sakataren harkokin wajen Amurka ya bayyana muhimmancin aiwatar da cikakken yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin tarayyar Habasha da dakarun Tigrai yayin wata doguwar tattaunawa da firaministan kasar Habasha. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Antony Blinken ya ce dole ne a dauki alhakin ta’asar da dukkan bangarorin suka aikata a cikin shekaru biyu da suka gabata, sannan a baiwa masu sa ido kan hakkin bil’adama damar shiga yankunan da fadan ya daidaita wanda aka kawo karshensa cikin watan Nuwamban da ya gabata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben Gwamna: APC ba ta da halastaccen dan takara a Taraba – PDP ta ankarar da INEC
Firaminista Abiy Ahmed ya ce mutanen biyu sun tattauna batun karfafa dangantakar da ta yi tsami a lokacin rikicin da ake yi tsakanin dakarun gwamnatin tarayya da abokansu na Eritriya da kuma ‘yan kabilar Tigrai.
Mista Blinken, wanda shi ma ya gana da jami’an Tigrai, ya ba da sanarwar karin tallafin dala miliyan 330 (£247m) ga Habasha.
A wani laabrin kuma, Henry ya yi hasashen kungiyar da za ta lashe gasar zakarun Turai
Tsohon kyaftin din Arsenal, Thierry Henry ya ce Manchester City ce za ta lashe kofin zakarun Turai na bana. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Henry ya yi wannan hasashen ne a lokacin da yake magana a gidan talabijin na CBS bayan an tabbatar da kungiyoyi takwas da suka fice a gasar.