Tsohon kyaftin din Arsenal, Thierry Henry ya ce Manchester City ce za ta lashe kofin zakarun Turai na bana. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Henry ya yi wannan hasashen ne a lokacin da yake magana a gidan talabijin na CBS bayan an tabbatar da kungiyoyi takwas da suka fice a gasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben Gwamna: APC ba ta da halastaccen dan takara a Taraba – PDP ta ankarar da INEC
A cewar fitaccen dan wasan kasar Faransa wanda ya taka leda a karkashin kocin City Pep Guardiola a Barcelona, yana jin cewa zakarun gasar Premier suna da abin da ake bukata don lashe gasar zakarun turai.
“Ina tsammanin kuma ina son City ta yi nasara.
“Ina tsammanin wannan lokaci ne da yakamata Pep ya lashe gasar”
“Ina son su yi nasara kuma ina ganin za su iya lashe ta,” in ji Henry.
A wani labarin kuma, Buhari ya taya Talban Katsina Murnar Cika Shekaru 80, Ya ce Ayi Koyi Da Shi
A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Ambasada Zakary Ibrahim, abokin karatunsa a kwalejin gwamnatin Katsina kuma tsohon darakta janar na hukumar leken asiri ta kasa, murnar cika shekaru 80 a duniya. Kamar yadda Daily Truat ta ruwaito.
Buhari a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar, ya yaba da jajircewa da sadaukarwar Ibrahim ga al’ummarsa ga Najeriya a matsayin Talban Katsina, tsohon mataimakin mai baiwa kasa shawara kan harkokin tsaro kuma karamin ministan harkokin waje.