Babban Alkalin Alkalan Jihar Kano, Mai Shari’a Nura Sagir, ya bayyana kaddamar da shirin samar da bayanan cin zarafin Mata a hukumance (SOD).
A cewar sa wannan na a matsayin wani mataki na dakile yawaitar cin zarafin mata a jihar Kano.
Mai shari’a Sagir ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da cibiyar tattara bayanan cin zarafin Mata a hukumance a Kano.
Ya ce laifin gallazawa rayuwar matan kullum karuwa yake, a don haka akwai buƙatar haɗin gwiwa tsakanin manyan masu fada aji da masu ruwa da tsaki.
A nasa jawabin, Grand Khadi na jihar, Dokta Tijjani Yakasai ya ce yawaitar Laifuka dake da alaka da cin zarafin mata abu ne mai ban tsoro, a don haka yai kira ga kowa da kowa da a tashi tsaye da nufin yakar wannan annoba.
Tun da farko, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya wakilta, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano a shirye ta ke na dakile duk wata barazana da ke addabar jihar.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta amince da samar da karin cibiyoyin tunkarar cin zarafin mata (SARC) a wasu masarautu hudu na jihar.