Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyar APC Asiwaju Tinubu ya zoyar Gwamnan jihar Kogi Yahya Bello a yau Juma’ar.
Yayin ziyarar Yahya Bello ya sauki Tinubun tare da karrama shi, duk kuwa da kashin da ya bashi a zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.
Yahya Bello Gwamnan Kogi dai na daga cikin yan takarar shugaban kasa da suka tsaya zaben fidda gwani a makon nan daya gudana a Abuja.
To har yanzu dai babu wata muhimmiyar magana kan makasudin ziyarar, duk da aka ganin cewa ba zai wuce yaje masa bane domin neman hadin kan sa.