Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APCn Kano sun amince a bada tikitin takarar Sanatan Kano ta Arewa ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kai tsaye ba tare da hamayya ba.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an cimma matsayar ne yayin taron masu ruwa da tsaki a APCn Kano da ya gudana a gidan gwamnati.
Gwamnan wanda zai kammala wa’adin mulkinsa a watan Mayu na shekara mai zuwa zai tsaya takarar Sanatan Kano ta Arewa.
Wata majiya ta bayyana cewa an aminta Ganduje ya tsaya takara ba tare da hamayya ba.
Yanzu haka dai Sanata Barau I Jibrin, (Maliya) shine akan wannan kujera kuma yana daga cikin wadanda suke neman kujerar Gwamna a zaben 2023.
Tuni kuma gwamnan ya bayyana mataimakin sa a matsayin wanda yake fatan ya gaje shi.
Comments 1