By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Asabar ne aka binne gawar dan jaridar Vanguard Tordue Salem a gidan iyalansa dake unguwar Gaado ta Mbayion a karamar hukumar Gboko ta jihar Benue.
Idan za’a iya tunawa dai an sanar da bacewar Salem ne a ranar 13 ga watan Oktoba, 2021 amma daga baya an gano gawarsa a dakin ajiye gawa na asibiti a Abuja a ranar 10 ga watan Nuwamba, 2021, lamarin da ya janyo cece-kuce da yawa.
An yi jana’izar marigayin ne a cikin jimami da hawayen masoyan su a wani biki daya samu halartar jama’a daga sassa daban-daban ciki har da uwargidan tsohon gwamnan jihar Benue, Misis Regina Akume.
Shugaban taron ‘yan jarida na jihar Benue da aka gudanar a Abuja, Dakta Emmanuel Anule, a warin taron jana’izar, yace kungiyar ta yi rashin wani jajirtaccen mamba wanda zai yi wahala a cike gudunmawarsa nan gaba kadan.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa har ila yau, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gboko/Tarka, DaktavJohn Dyegh, wanda ya wakilci kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana rasuwar Salem a matsayin abin bakin ciki da takaici.
Dyegh yace majalisar dokokin kasar ba za ta daina yin komai ba domin ganin ta bankado al’amuran da suka dabaibaye mutuwar marigayin dan jaridan duk da ya jajanta wa ‘yan uwa tare da yin addu’ar Allah ya basu kwarin guiwar jure rashin da ba za a iya kwatantawa ba.
Tun da farko a wani taron buƙatu, wani limamin cocin Katolika na Kastina-Ala ya umarci Kiristoci dasu yi shiri don saduwa da Ubangiji a duk lokacin da aka kira su.
Comments 1