Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Femi Fani Kayode ya roki Gwamnatin Tarayya da ta gano tare da kama masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci a Najeriya.
Ya ce dole ne ‘yan Nijeriya su hadu ba tare da la’akari da duk wani bambance-bambancen da ke tsakaninsu ba, su kuma tsaya kyam ga ‘yan kasashen waje da ke da niyyar kawo wa kasar nan tarnaki da kuma kashe ‘yan kasa da ba su ji ba gani ba, musamman a Arewacin Najeriya.
Jigon na APC ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar jajantawa jihar Zamfara kan kashe-kashen da aka yi kwanan nan a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum.