Magoya bayan kwallon kafa na kasar Sin za su bukaci fitar da kudi har dala 680 don ganin Lionel Messi.
Messi dai shine dan wasan da zai jagoranci Argentina da Australia a wasan sada zumunta na Beijing, in ji masu shirya gasar.
KU KARANTA: Matsalar Tsaro: Gwamnan Kaduna Sanata Uba Sani Ya Gana Da Shugabannin Tsaron Jihar
Wasan da za a yi ranar 15 ga watan Yuni a filin wasa na ma’aikata mai daukar mutane 68,000, wasa ne na karawar Argentina da Australia a zagaye na 16 na gasar cin kofin duniya na Qatar.
Messi, wanda ke shirin barin Paris Saint-Germain a bana, ya zura kwallo a ragar Argentina da ci 2-1, kuma sun tashi gasar cin kofin duniya.
Masu shirya gasar sun ce za a fara siyar da tikitin daga yuan 580 ($82) zuwa yuan 4,800 a kashi na biyu, a ranakun 5 da 8 ga watan Yuni.
Magoya bayan dan wasan dake son siyen tikiti ta yanar gizo, sun koka kan yadda farashin tikitin ya tashi cikin kankanin lokaci.
Wannan dai ita ce ziyarar farko da Messi zai kai kasar Sin tun daga shekarar 2017.
Ana ɗaukar matakai masu tsauri don hana ɓarna, inda ake buƙatar ƴan kallo su ba da bayanan tantancewa da nuna katin shaida ko fasfo don shiga filin wasan.
A wani labarin kuma: Tauraron Dan Wasan Arsenal Bukayo Saka Ya Ziyarci Legos
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da kasar Ingila, Bukayo Saka ya samu tattaunawa da mutane da dama bayan ya yada hoton bidiyonsa a ziyarar da ya kai birnin Lagos babban birnin kasuwancin Najeriya.
DIMOKARADIYYA ta rawaito cewa Saka ya kasance a unguwar Bariga da ke Legas ranar Alhamis.