An cafke dalibai biyu a Zamfara kan yunkurin sa ce Shugaban Makarantar Sakandire
Yan sandan Zamfara sun cafke dalibai guda biyu kan yunkurin sa ce shugaban makarantun sakandire guda biyu daban-daban dake Jahar.
Mista Rabi’u Hussaini Kwamishinan Ƴansandan Jahar Zamfara yake bayyana haka ga manema labarai, ya ce “mun sami rahoto daga kwalejin gwamnatin tarayya dake Anka da kuma Makarantar Dominican dake Gusau.”
KARANTA:-Jami’an tsaro sun hallaka kasurgumin Dan ta’adda a Jahar Kogi
Rabi’u Hussaini yace ” A ranar 25 ga watan Yuni 2021 muka sami sako a takadda a cikin akwatin korafi dake Sha’iskawa a Gusau.
Takadda ta kunshi shiri kan yadda za’a sace shugaban makarantar Rev. Chinyere da kuma wasu dalibai.
Dajin haka Yan sandan suka bazama don gano suwa ke da hannu a ciki, in da suka cafke Donatus Eje wanda shugaban makarantar take zargi.
Kwamishinan yace “a lokacin da Donatus Eje ya ke amsa tambayoyi an gano dan aji uku ne a sakandire.”
Yace “zamu cigaba da bincike don zakulo abokan aikinsa.”
Kwamishinan Rabi’u Hussaini ya cigaba da cewa “A ranar Alhamis Shugaban makarantar FGC Anka ta kawo korafi ga Ƴansandan tana cewa wani ya kira ta yana mata barazana da ta bashi miliyan uku ko kuma zai dauke ta tare da wasu dalibai.”
Kwamishinan Ƴansandan yace “dajin hakan sai muka bazama don gano waye ya aikata hakan, in da suka cafke Tukur Bashir Dan Karamar Hukumar Bunkure”
Bayan amsa tambayoyi an gano Tukur Bashir dan aji daya ne.
Dan sandan yace “Kawo yanzu dai mun cafke sama da mutane arba’in da biyar da lafin barazana ta tada zaune tsaye.”