Jami’an tsaro sun hallaka kasurgumin Dan ta’adda a Jahar Kogi
A wajan musayar wuta da Yan bindiga, Yan sakai da mafarauta sun hallaka wasu kasurguman Yan ta’adda guda biyu dake addabar Karamar hukumar Olamaboro dake Jahar Kogi.
Rundunar Yan sakan da mafarautan na daga cikin sabbin jami’an tsaro da aka samar don yaki da Yan ta’adda a Jahar.
Shugaban Karamar hukumar Olamaboro, Adejoh Friday Nicodemus ya assasa rundunar don kawo karshen ta’adanci dake addabar yankin.
KARANTA:-An wargaza mutum-mutumin sarauniyar Ingila a Kasar Canada
Kamar yadda rahotanni ke zuwa daya daga cikinsu sunan sa Lawal Isa wanda aka fi sani da Osama dan asalin yankin Ofugo Okpo, a inda sauran aka cafke su sannan aka damka su zuwa mahukunta.
CPS ya bayyana cewa gwamanti a kowane mataki zata cigaba da kawo hanyoyi don kawo karshen ta’adanci dake addabar Jahar Kogi.