Kwamishinan yada labarai na jihar Edo, Chris Nehikhare, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke daya daga cikin wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne da hannu wajen yin garkuwa da fasinjoji 32 a tashar jirgin kasa ta Igueben.
Nehikhare ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin Benin a karshen mako.
KU KARANTA: Rikicin PDP A Kano Na Neman Daukar Sabon Salo
Kwamishinan ya kara da cewa daya daga cikin wadanda ake zargin ya gujewa sansanin masu garkuwa da mutanen, wanda hakan ya bashi damar fitowa kuma aka kama shi.
Ya kuma yi alkawarin tallafa wa jami’an tsaro domin dakile sake afkuwar irin wannan lamari a jihar.
Bayan da aka yi garkuwa da mutane 32, jami’an tsaro da mafarautan yankin sun fantsama tare da tseratar da dajin da kuma binciko masu hannu da tsaki kan wannan aika-aika.
A wani labarin kuma: Zamu Kubutar Da Fasinjojin Jirgin Kasan Edo Cikin Koshin Lafiya – FG
Gwamnatin tarayyar Najeriya a ranar Lahadin nan, ta bayyana sace fasinjojin jirgin kasa a tashar jirgin kasa ta Tom Ikimi, Igueben, Edo, a matsayin abin kyama da nuna hali na Allah wadai.
Mista Henshaw Ogubike, Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Sufuri ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.