…Karya ce – Mai magana da yawun yakin neman zaben PDP
Ana ci gaba da mayar da martani dangane da ziyarar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ke yi a kasar waje.
Wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta rawaito cewa an dauki tsohon mataimakin shugaban kasar ne a ranar Lahadi daga birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa zuwa birnin Landan na kasar Birtaniya domin jinya.
KU KARANTA KUMA Zamu Kubutar Da Fasinjojin Jirgin Kasan Edo Cikin Koshin Lafiya – FG
Atiku baya jin dadi; yana asibiti yana karbar magani. Shi ya sa bai dawo Najeriya don yakin neman zaben shugaban kasa ba.
“Ya kasance a Dubai amma yanzu ya bar Dubai zuwa Landan don jinya. An garzaya da shi kasar Birtaniya domin yi masa magani. Shi ya sa har yanzu yake kasar waje.” Tabloid ya ruwaito wata majiya ta PDP da ba a bayyana sunanta ba tana cewa.
Kakakin majalisar kamfen din PDP, ya yi watsi da rahoton inda ya bayyana shi a matsayin abin dariya na shekara.
Da yake mayar da martani ga jaridar ta yanar gizo, mai baiwa Atiku shawara kan harkokin yada labarai, Mista Paul Ibe, ya ce dan takarar na PDP zai isa Landan ranar Litinin, duk da cewa ya yi watsi da rahoton rashin lafiyar.
Da yake bayyana hakan a shafin sa na Twitter @omonlakiki, Ibe ya ce, “Don kauce wa shakku, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya (1999-2007) zai isa Landan ranar Litinin, 9 ga watan Janairu domin ganawa a ranar Talata da Laraba bisa goron gayyatar gwamnatin Burtaniya.”
Shima da yake jawabi, Daraktan, dabarun sadarwa, Kwamitin Gudanar da Zabe na Majalisar Kamfen na PDP, Dele Momodu, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da rahoton gaba dayansa “saboda gaba daya karya ce.”
A wata tattaunawa ta wayar tarho da jaridar PUNCH, Momodu ya ce, “Mutumin ya tafi hutu. Duk wanda ya san shi zai iya gaya maka cewa mutumin (Atiku) ba ya wasa da hutunsa.
A Wani Labarin Kuma An Cafke Guda Cikin Wadanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Fasinjojin Jirgin Kasa
Kwamishinan yada labarai na jihar Edo, Chris Nehikhare, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke daya daga cikin wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne da hannu wajen yin garkuwa da fasinjoji 32 a tashar jirgin kasa ta Igueben.
Nehikhare ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin Benin a karshen mako.