An Haramtawa Blessing Okagbare tauraruwar gasar tsallen-badake ta Najeriya, wadda ta ci lambar azurfa a gasar Olympics a 2008, wasa tsawon shekara 10 saboda laifin amfani da abubuwan kara kuzari.
Wata sanarwa da Kotun tabbatar da adalci a harkar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta fitar a yau Juma’a ce ta tabbatar da hakan.
An kori Blessing mai shekara 33, wadda kuma tana shiga gasar tsere, daga gasar Olympics a Tokyo a shekarar da ta wuce, 2021, kafin tseren kusa da karshe na mita 100 na mata bayan da wani gwaji da aka yi mata a Slovakia ranar 19 ga watan Yuli ya gano ta yi amfani da abubuwan kara kuzari.
Kotun ta ce hukuncin ya fara ne daga ranar 31 ga watan Yuli, 2021.
Hukuncin ya kuma zartar da cewa duk wani sakamako da lambobin da makida kudin da ta samu na halartar duk wata gasa daga 20 ga watan Yuni 2021 a karbe su.
A watan Oktoba ne dai aka tuhumi, Okagbare da laifuka uku na saba dokokin amfani da abubuwan kara kuzari, wadanda ta musanta gaba daya.