An fara kaɗa ƙuri’a a Anambra
An fara kada kuri’a a jihar Anambra domin zaben ‘yan majalisar dokoki.
DAILY POST ta rahoto cewa a garin Awka, babban birnin jihar, an fara kada kuri’a da karfe 8:30 na safe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Wasu Dattawa, Malamai, Kiristoci Sun Zaɓi Uba Sani A Matsayin Ɗan Takarar Su
Kwamishiniyar zabe ta jihar, Misis Elizabeth Agwu, a wata ganawa da manema labarai a ranar Juma’a, ta ce hukumar ta shirya, kuma za a fara kada kuri’a da wuri.
Binciken ya kuma nuna cewa BVAS ta na da sauri musamman wajen kama masu kada kuri’a.
A wani labarin kuma:Hukumar NHRC Ta Nuna Damuwarta Kan Kalaman Tunzura Jama’a
Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa NHRC ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun karuwar kalaman nuna kiyayya a fadin kasar nan, sakamakon yadda ‘yan siyasa ke neman goyon baya a fannin siyasa. Kamar yadda Punch ta ruwaito.
Wannan a cewar hukumar ya sanya ake amfani da kabilanci da addini wajen haifar da rarrabuwar kawuna, tsoro da kuma kiyayya a tsakanin kungiyoyi daban-daban.