Zaɓe: Hadiman Gwamnan Katsina guda uku sun mutu a hatsarin mota
Wasu hadimai uku ga Gwamnan Jihar Katsina sun mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a daren Juma’a yayin da suke kan hanyarsa ta zuwa mahaifar Gwamna Aminu Masari, Kafur, inda ake sa ran zai kada kuri’a a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki da za a yi a ranar Asabar 19 ga watan Maris.
Al-Amin Isa, Darakta Janar na Sabbin Kafafen Yada Labarai, wanda ya tabbatar da hakan, ya ce hadarin ya afku ne a wani kauye mai suna Gadar Tsuntsaye kusa da Jikamshi a karamar hukumar Musawa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Hukumar NHRC Ta Nuna Damuwarta Kan Kalaman Tunzura Jama’a
Isah ya bayyana sunayen wadanda aka kashe a lamarin kamar haka: Nura Sufayanu da Kabir Ali, yayin da Amadu Ali kane ne ga Gwamna.
Isah ya kuma ce wasu mutane uku sun jikkata a hadarin kuma suna karbar kulawa a babban asibitin Malumfashi.
A wani labarin kuma:An fara kaɗa ƙuri’a a Anambra
An fara kada kuri’a a jihar Anambra domin zaben ‘yan majalisar dokoki.
DAILY POST ta rahoto cewa a garin Awka, babban birnin jihar, an fara kada kuri’a da karfe 8:30 na safe.