Ƴan Ta’adda a ranar Alhamis sun kai kai hari a wata barikin Soji a Niger, inda suka ƙone ta tare da faɗa tsakanin su da Sojojin.
Wani Shugaban Matasa a Karamar Hukumar Shiroro Sanni Yusuf Kokki ya bayyana haka a cikin sanarwar daya rarraba wa Manema labaru a ranar Juma’a, yana mai cewa ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun tafi da motocin sintiri da kayayyakin abincin su.
“A lokacin artabun, bayan mayaƙan sun cinnawa Makarantar Sakandire ta Allawa wuta, wanda take a matsayin barikin sojin, sun kwashe kayayyakin yaƙi, da motocin sintiri, gami da kwashe kayayyakin abincin da sauran su,”inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari ya taya Amaechi murnar samun sarauta a Daura
Ya ƙara dacewa ƴan ta’addan da muggan makamai sun kuma zo garin tare da bada himma ga Sojojin.
“Dayake tabbatar da rahoton dake fitowa daga Al’ummar Allawa, Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jahar Niger, yayi nuni dacewar, ƴan ta’adda dauke da muggan makamai na zamani sun zo garin inda suka tafi kai tsaye wajen sojojin, tare da yi masu kwantan ɓauna da suke zaune a garin,” inji sanarwar ta bayyana.
Dayake jawabi a wayar tarho da wakilin Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta The PUNCH, Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Tsaron Cikin gida Emmanuel Umar ya Tabbatar da kai harin, yace an yi faɗa, amma babu mutuwa.
Yace an ƙone sansanin Sojin,amma saboda anyi musayar wutar tsakanin Sojoji da Maharan.
Comments 1