An gano Ɗaruruwan Makarantun Bogi da akayi rajista don ciyar da Ɗalibai a Nasarawa
Akalla makarantun bogi 349 da aka yi rajistar shirin ciyar da yara a jihar Nasarawa ne tawagar kwamitin gwamnatin tarayya ta fallasa.
Shugaban tawagar kwamitin kuma mai ba wa Ministan Agaji, Malam Abdullahi Usman shawara,
ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci tawagar ‘yan kungiyar zuwa gidan gwamnati dake Lafiya, domin kai ziyarar ban girma ga gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da duminsa: ADC ta kori Ɗan Takarar ta na Shugaban Ƙasa, Kachikwu
Usman, yayin da ya yi zargin cewa wasu daga cikin jami’an na karkatar da kudaden da aka ware don shirin ciyar da makarantu a jihar, ya ce an kama makarantun firamare na gwamnati 1,203 a matsayin makarantun da suka amfana a lokacin da aka fara shirin.
Ya ce bayan tantancewar, “kwamitin ya gano makarantun bogi 349 tare da wasu jami’ai sun sanya aljihun kudin da aka ware domin ciyar da daliban wadannan makarantun.”
“Bayan gano hakan, manyan jami’an ma’aikatar a Abuja sun ba da shawarar a cire jihar Nasarawa daga cikin shirin, amma domin kada a hukunta yaran talakawa a kan hukuncin da bai dace ba, kwamitin ya yi watsi da shawarar,” in ji Usman.
Sai dai Usman ya bayyana cewa an dakatar da jami’in shirin da mai bada shawara na jihar Nasarawa tare da maye gurbinsu.
Ya kuma yabawa masu ruwa da tsaki na shirin bisa tabbatar da nasarar shirin a jihar.
Daga cikin su akwai: Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA), masu yi wa kasa hidima (NYSC), National Bureau for Statistics (NBS), da ma’aikatar ilimi ta jiha, da dai sauransu.
Shugaban tawagar Nasarawa ya kuma yaba da irin goyon bayan da Gwamnan ke yi
A wani labarin kuma: Gwamnatin Tarayya na kokarin hana ƴaƴan talakawan Najeriya Ilmi – NANS ta koka
Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta zargi gwamnatin tarayya da shirin daukar ilimi daga hannun talakawa zuwa ga masu kuɗi.
Kungiyar daliban ta ce gwamnati mai ci ta gaza ta kowane fanni, inda ta kara da cewa “da tuni an kori gwamnati mai ci.
Hukumar ta kuma kada kuri’ar rashin amincewa da gwamnatin shugaba Mohammadu Buhari