Ni ba kamar Yahaya Bello bane – Inji Wike
Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya yi kakkausar suka a ranar Juma’a a lokacin da ya ce shi ba kamar takwaransa na Kogi, Yahaya Bello ba ne.
Ya yi magana ne a wajen kaddamar da wani littafi mai suna “Zababbun Hukunce-hukuncen Kotun Daukaka Kara da Kotun Koli,” wanda Mai Shari’a Abdu Aboki mai ritaya ya rubuta, inji rahoton
KARANTA WANNAN LABARIN: Da duminsa: ADC ta kori Ɗan Takarar ta na Shugaban Ƙasa, Kachikwu
Wike ya ce ziyarar da ya kai babban birnin kasar ta tuna masa shan kayen da ya sha a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar PDP a watan Mayu.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan ne karon farko a Abuja bayan ya rasa tikitin PDP a hannun tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
“Lokacin da na sauka na wuce wurin taron, na ce ina tsammanin Ubangijina ya so ni da gangan in tuna 28 da 29 ga Mayu na abin da ya faru.”
Wike ya ce ba kamar Bello da ya ziyarci Abuja da dama tun bayan rasa tikitin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba, ya ci gaba da zama a jiharsa.
“Ba ni kamar Yahaya Bello wanda ya yi rashin nasara yana zuwa Abuja kullum,” in ji shi.
Shugaban Ribas ya yaba da yadda mai shari’a Aboki ya jajirce wajen kare adalci da bin doka da oda.
A wani labarin kuma: An gano Ɗaruruwan Makarantun Bogi da akayi rajista don ciyar da Ɗalibai a Nasarawa
Akalla makarantun bogi 349 da aka yi rajistar shirin ciyar da yara a jihar Nasarawa ne tawagar kwamitin gwamnatin tarayya ta fallasa.
Shugaban tawagar kwamitin kuma mai ba wa Ministan Agaji, Malam Abdullahi Usman shawara,
ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci tawagar ‘yan kungiyar zuwa gidan gwamnati dake Lafiya, domin kai ziyarar ban girma ga gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule.