An gano wata ‘yar Chibok da Boko Haram suka yi garkuwa da ita, mai suna Hauwa Joseph.
Rundunar sojojin Najeriya ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis.
“Yarinyar wacce akayi garkuwa da ita tare da yan matan Chibok da an kanta da jaririnta a halin yanzu suna wani asibitin sojoji,” in ji sanarwar.
An gano tsohowar wadda akayi garkuwan da ita ne a lokacin wani samame da rundunar sojin kasar nan ta kai a Arewa maso Gabas a ranar 14 ga Yunin, shwkarar 2022.
An sace Hauwa da abokan karatun ta ne a ranar 14 ga Afrilun shekarar 2014 daga makarantar sakandaren mata ta gwamnati da ke garin Chibok a jihar Borno.
Sama da dalibai 270, galibinsu kanana ne, aka kwashe su, kuma aka kai su cikin dajin a cikin ayarin motocin mayakan Boko Haram
Yayin da aka samu mutuwar mutane da dama ko kuma aka gano, an kiyasta cewa akalla yammata 100 na Chibok ne har yanzu ba a gansu ba.
A cikin makon da ya gabata ne, sojojin na rundunar ta 26 Task Force Brigade da ke kai farmaki a Ngoshe sukaci karo da daya daga cikin ‘yan matan.
Kamar Hauwa, an same Mary Dauda mai shekara 27 da yaro a hannunta
Comments 1