Dalilan da suka sanya na Janye wa Tinubu — Amosun
Tsohon Gwamnan Jahar Ogun Sanata Ibikunle Amosun yace nuna goyon baya da Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta APC tayi, na Ɗan Takara daga yankin Kudu Maso Yamma, ya sanya ya janye wa Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Amosun da sauran ƴan Takara daga yankin Kudu, ciki har da Gwamnan Jahar Ekiti Dr. Kayode Fayemi da tsohon shugaban Majalisar Wakilai Ta Ƙasa Dimeji Bankole sun janye wa Tinubu a Babban taron APC daya wakana a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: DA DUMI-DUMI: Zanga-Zangar Kinjinin Shugaban Jam’iyar APC Na Kasa Ta Barke A Sakatariyar Jam’iyar Dake Abuja
Tsohon Gwamnan ya bayyana haka a ranar Alhamis a lokacin da yake jawabi ga Magoya Bayan sa, da suka fito daga dukkanin Ƙananan Hukumomi na Jahar a Alake Palace Dake Abeokuta.
Amosun wanda ya yiwa Magoya bayan sa jawabi a harshen Turanci da Yarbanci, yace bai damu dole sai ya zama Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar ba.
Yace yana da ra’ayi ne kashi 20, a yayin da ya bada sauran kashi 80 na so ga ƴan yankin Kudu Maso Yamma da Najeriya.
A cewar sa, a lokacin da nake da ra’ayin neman kujerar shugaban ƙasa shekaru biyu da suka gabata, na gayawa magoya baya na cewa zan nemi takarar da ra’ayi kashi 20, zan kuma goya ma kowa ye Jam’iyyar ta tsaida.