Bayan harin yan bindiga jan gidan yarin Kuje, yanzu haka an gaza ganin fuskokin wasu manyan mutane a najeriya.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa lamarin yafaru ne daren jiya Talata, inda bayan fashwar wani abu, aka fara jiyo harbe harben bindiga.
Musayar wutar dai rahotanni sun tabbatar da cewa ta faru tsakanin jami’an tsaron gidan gyaran halin, da kuma bata garin.
Daga cikin wadanda aka gaza ganin su sun hadar da Dan sandan nan Abba Kyari, sai kuma tsohon gwamnan Filato, Joshua Dariye, da takwaransa na Taraba Jolly Nyame.
Har kawo yanzu dai babu wani martini daga bangaren gwamnatin tarayya, dangane da wannan batu, duk da cewa mai magana da yawun hukumar kula da gidajen yarin ya tabbatar da faruwar lamarin.
Wani shaidar gani da ido ya shaidawa Jaridar The Nation, suna zargin da dama cikin wadanda ake tsare da su a wannan gidan gyaran hali ne suka tsere.
To sai dai wata majiya ta bayyana cewa an kwashe mutanan ne don basu kariya, domin gudun me kaje yazo.