Hukumomin kasar Saudiyya sun sanar da sake dage lokacin dakatar da shiga da maniyyatan aikin hajjin bana cikin kasar.
Wata Sanarwa da aka rabata ga manema labarai ta hannun hukumar NAHCON a Najeriya, ta ce wannan wata dama ce ga alhazai kasar 3000, wadanda ke dakon akai su kasar ta Saudiyya.
Shugaban hukumar Alhaji Zikrullah Hassan ya ce an samu karin wa’adin ne, bayan wata tawaga ta musamman daga Najeriya bisa jagorancin sa, suka tattauna ta fahimtar juna a tsakanin su, kuma a karshe suka fahimci juna.
Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa maniyyatan Najeriya na bana, na cike da zullumi sakamakon yadda ake ci gaba da samun tsaiko wajen jigilar ta su.
A baya dai wata ƙididdiga ta nuna cewa kusan maniyyatan 5000 daga Najeriya ne, baza su samu damar gudanar da aikin hajjin bana, duk da cewa hukumar NAHCON ta bayar da tabbacin yin duk mai yiwuwa wajen ganin maniyyatan kasar baki daya sun shiga Saudiyya.
A cewar Zikrullah karin wa’adin da akai yanzu haka, kamfunan jiragen sama na Max Air, da Azman ne zasu karasa aikin jigilar maniyyatan.