An gurfanar da wani dan jarida a jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin Najeriya, Nengi Owei-Ilagha a gaban babbar kotun tarayya da ke Yenagoa a ranar Litinin bisa zarginsa da yin wani rubutu na batanci a shafin Facebook kan wani dan kwamitin hulda da ‘yan sanda a jihar.
An bayyana mamban kwamitin huldar ‘yan sandan a matsayin Emmanuel Chiefson.
KU KARANTA KUMA Wani Dan Jaridar BBC Ya Sha Na Jaki Yayin Daukar Rahoto
Jaridar DIMOKURADIYYA ya rawaito cewa kwamishinan ‘yan sanda, Ben Okolo ya shigar da karar dan jaridar kan tuhume-tuhume uku a gaban alkali Emmanuel Gakko.
Sai dai wanda ake tuhumar Mista Owei-Ilagha, ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Lauyan sa, Godfrey Otiotio, ya gabatar da bukatar neman beli. Ya ce tun da farko ‘yan sanda sun bayar da belin wanda ake kara kuma a shirye yake ya gabatar da kansa domin yi masa shari’a.
Da yake magana kan aikace-aikacen, lauyan masu gabatar da kara, M.Y. Benabo, ya ce ba ya adawa da belin. Sai dai ya roki kotun da ta bukaci wanda ake kara da kada ya yi tsokaci a shafukan sada zumunta da za su iya bata sakamakon shari’ar.
Lauyan da ake kara, Mista Otiotio, ya yi alkawarin cewa wanda yake karewa ba zai yi wani tsokaci dangane da lamarin ba a shafukan sada zumunta.
Da yake yanke hukunci kan neman belin, alkali ya bada sharadin belin dan jaridar kan Naira miliyan daya da kuma mutum daya da zai tsaya masa.
Mista Gakko ya ce kafafen yada labarai na taka rawa kuma suna ci gaba da taka rawar gani a cikin al’umma amma ya yi maraba da cewa bai dace kafafen yada labarai su rika tantance sakamakon shari’o’in da ke gaban shari’a ba. (NAN)/Solacebace
A Wani Labarin Kuma Johnathan Yayi Kiran A Gudanar Da Bincike,A Gurfanar Da Masu Aikata Laifukan Siyasa a Najeriya
Tsohon shugaban kasa Goodluck Johnathan ya yi kira ga jami’an tsaro a Najeriya da su tabbatar da bayanan da suka dace, da bincike domin gurfanar da masu aikata laifuka da bata gari da ke fakewa da siyasa domin su zama tarnaki ga wasu.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a shekarar 2015, wanda ya amince da shan kaye a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari domin samar da zaman lafiya a Najeriya, ya yi wannan kiran ne a lokacin kaddamar da gadar Afi-Uko Ntighe mai tsawon kilomita 1.15 a karamar hukumar Mbo a jihar Akwa Ibom a jiya.