Wani dan jaridar BBC ya ci na jaki sannan ‘yan sanda sun damke shi bayan ya je daukar rahoto kan zanga-zangar da aka yi a Shanghai a ranar Lahadi, 27 ga watan Nuwamba.
KU KARANTA: An kori wani jami’in ‘yansanda daga aiki bayan ya lakaɗawa wani na jaki
Ed Lawrence yana hannun jami’an tsaro a garin inda rike shi na awoyi da dama kafin su sake shi. BBC ta bayyana cewa:
“BBC ta shiga damuwa mai yawa kan yadda aka azabtar da dan jarida Ed Lawrence wanda yaje daukar rahoto kan azabtar da dan jaridarmu Ed Lawrence da aka yi yayin da aka kama shi sannan aka sanya masa ankwa a Shanghai.”
“An rike shi na tsawon awoyi kafin a sake shi. Yayin da aka kama shi ya ci duka tare da hambari a hannun ‘yan sanda. Kuma an yi masa hakan ne yayin da yake kan aikinsa.”
Kakakin ma’aikatar harkokin kasashen ketare, Zhao Lijian ya ce batun BBC ba haka bane, bai bayyana cewa shi ma’aikacin jarida bane ko ya nuna wata alamar hakan.
Ya ce jami’an tsaro sun bukaci kowa ya tafi inda wasu su ka ki bayar da hadin kai, hakan yasa aka janye su daga wurin.
Mai goge-goge ya ci na jaki a hannun matashin da ya ritsa da yana lalata da budurwa a bayin da zai wanke
Wani mutum ya kai wa mai goge-goge farmaki yayin da ya kama shi yana lalata da wata mace a bayi, LIB ta ruwaito.
Mutumin mai suna Billy Dean Fallon, mai shekaru 28 yana tsaka da lalata da wata mata sai mai goge-goge ya fara kwankwasa kofar bayin, nan da nan ya fito ya fara dukan mai goge-gogen.
Yayin da aka gurfanar da shi a gaban kotu, a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba, ya amsa laifinsa. Hakan yasa aka umarce shi da biyan mai goge-gogen $1,500.