Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta haramta amfani da buhunan ‘Ghana Must Go’ da fasinjoji ke yi a dukkan filayen jiragen saman kasar.
A wata sanarwa da FAAN ta fitar mai taken, ‘Re: Prohibition of Use Of Ghana Must Go’, mai dauke da sa hannun Manaja, Ma’aikatar Jiragen Sama, Henok Gizachew, ta ce haramcin ya shafi fasinjojin da ke bi ta filayen jiragen sama na kasa da kasa.
Karanta nanMutane Hudu Sun Rasa Rayukan Su Bisa Zargin Amfani da Maganin Kanjamau Na Gargajiya
Gizachew ya bayyana cewa hukumar ta hana amfani da buhun ne saboda ya jawo hasarar da kamfanonin jiragen sama suka yi da kuma lalata na’urar daukar bel na filayen jiragen sama.
Ya lura cewa fasinjojin da ke son yin amfani da ‘Ghana Must Go’ don yin balaguro suna janyo lalacewar wasu naurori masu tantance kaya a filayen jiragen saman Nijeriya.
An alakanta amfani da jakunkunan ‘Ghana Must Go’ da lalacewar na’urorin jigilar dakunan jiragen sama na kasar da dama da kuma wanda ya jefa makudan kudade a wuyan hukumar ta filin jirgin.
A wani labarin kumaBam Ya Tashi Da Yan Boko Haram 4 A Borno
Wasu gungun ‘yan ta’addan da suka kai hari a yankin San San da ke karamar hukumar Mobbor a jihar Borno sun kashe kansu sakamakon fashewar wani abin fashewa.
LEADERSHIP a ranar Juma’a ta tattaro cewa bam din ‘yan ta’addan ya tayar da su ne a lokacin da suke dasa bama-bamai a kusa da titin sojojin na Birged 5 a ranar Laraba, inda suka farfasa gawarwakinsu.
A halin da ake ciki, sojojin MNJTF Sector 4 da aka tura a Chetima Wongonu sun gano wani bam a kusa da kauyen Chetimari.