Wasu gungun ‘yan ta’addan da suka kai hari a yankin San San da ke karamar hukumar Mobbor a jihar Borno sun rasa ransu sakamakon fashewar wani abin fashewa dake hannunsu,ana kuma kyautata zaton ‘yan ta’adda hudu na kungiyar IS da ke yankin yammacin Afirka ne.
LEADERSHIP a ranar Juma’a ta tattaro cewa bam din ‘yan ta’addan ya tayar da su ne a lokacin da suke dasa bama-bamai a kusa da titin sojojin na Birged 5 a ranar Laraba, inda suka farfasa gawarwakinsu.
Karanta nanMutane Hudu Sun Rasa Rayukan Su Bisa Zargin Amfani da Maganin Kanjamau Na Gargajiya
A halin da ake ciki, sojojin MNJTF Sector 4 da aka tura a Chetima Wongonu sun gano wani bam a kusa da kauyen Chetimari.
Ya ce,wasu da ake zargin ‘yan ta’addar ISWAP ne suka bude wuta a Chetimari da daddare, tare da fatan za su sa sojojin su shiga cikin bama-baman.
Duk da haka, sojojin sun yi turjiya kuma daga baya sun gano IEDs da misalin karfe 6:30 na yamma kuma daga baya aka ciro su” in ji shi.
A wani labarin kumaZaben 2024: Mataimakina Yana da Damar Tsayawa Gakara – Gwamna Obaseki Ya Magantu
Wani kwararre a fannin yaki da masu tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya tattaro cewa, duk da munanan hare-hare da aka yi a fagen fama da asarar yankuna da kayayyaki da ma’aikata, ‘yan ta’addan sun zafafa amfani da bama-bamai.
Yin amfani da dabarar bama-bamai wajen kare wuraren abokan gaba da kuma yin kwanton bauna a layin sadarwa na iya ci gaba, kuma, a wasu sassan, ya zama hanya daya tilo ta yaki yayin da Boko Haram ke kara kasa yin manyan hare-hare.