A ranar Asabar din nan ne aka kashe wani da ake zargi da satar akwatin zabe a karamar hukumar Anyigba ta jihar Kogi yayin da jami’an tsaro suka dauki matakin dakile shirinsa na kawo cikas a zaben da ake cigaba da gudanarwa a jahar.
Har yanzu dai ba a tabbatar da ko wanene marigayin da kuma jam’iyyar siyasar da ake zargin ya yi wa aiki ba.
Karanta nanGwamna Dauda Ya Nuna Damuwa Akan Halin Da Gidan Gyaran Halin Gusau Yake Ciki
Ba a fayyace cikakken bayani kan ko jami’an tsaro ne suka harbe mutumin ko wasu maharan da ba a san ko su waye ba.
Kungiyar Transition Monitoring Group (TMG) ta ruwaito lamarin a shafinta inda ta bayyana cewa an harbe wanda ake zargi da hannu a rikicin siyasar da yayi yunkurin kawo cikas a zaben ta hanyar kwace akwatin zabe a karamar hukumar Anyigba ta jihar Kogi.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa a lokaci guda ana gudanar da zaben gwamna a jihohin Kogi, Bayelsa, da kuma Imo.
A shekarun baya ne tsohon shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya saka hannu akan dokar gani da harbi akan duk wanda yayi yunkurin satar ajwatin zabe a lokacin da ake gudanar da zabe.
A wani labarin kuma
Kuskuren Na’ura Ya Sa Bashin Da Muke Bin Kwastomominmu Ya Goge–MTN
Kamfanin sadarwa na MTN ya bayyana cewar matsalr na’ura ce tasa basussukan da suke bin kwastomominsu suka bace ba tarw da an gansu ba.
Kamfanin ya bayyana cewar babu gaskiya akan maganar da ake cigaba da yadawa cewar Kamfanin ya yafe wa dukkanin wadanda yake bi bashin katin kiran waya ko Data.