Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana bakin cikinsa kan halin makarantar gyaran tarbiyar yara yake ciki a jahar.
Gwamnan ya bayyana rashin jin dadinsa ne a lokacin da ya ziyarci wata makarantar da aka amince da ita, wadda aka kafa domin zama cibiyar gyaran tarbiyya musamman a tsakanin yara masu karancin shekaru.
Lawal ya dora laifin dambarwar da ke faruwa a makarantar a kan rashin kulawar da gwamnatin da ta shude ta yi, ya kuma yi Allah wadai da irin kazantar da makarantar ke ciki.
Karanta nanKuskuren Na’ura Ya Sa Bashin Da Muke Bin Kwastomominmu Ya Goge–MTN
Ya yi nuni da mugun warin da ke fitowa daga wasu sassan dakin kwanan dalibai, da fashe-fashen tagogin da aka yi a makarantar, da fashe-fashen bango da tarkacen benaye yana mai cewa wasu daga cikin daliban na kwana a kan tsofaffin katifu.
Gwamnan wanda a zahiri ya damu da halin da makarantar ke ciki ya zagaya domin duba kicin, dakunan taron karawa juna sani da sauran sassan makarantar.
Na zo ne don in gani da kaina halin da wannan wuri yake ciki amma abin da na gani ya zuwa yanzu abin ban tsoro ne ba ma zan iya bayyanawa ba.
Wurin da ya kamata ya zama cibiyar da ta dace domin gyara munanan dabi’un yara yana cikin yanayin da ba za a iya ajiye dabba ba balle dan Adam.
Babu wani dattijon da ke da alhakin kai yaronsa cikin yanayi mara kyau duk da tsananin halinsa na rashin ji in ji Gwamnan.
A wani labarin kumaGwamnatin Jahar Katsina Ta Haramta Duk Wani Babban Taron Jama’a A Cikin Dare
Tun da farko, shugaban makarantar, Sale Muhammad wanda ya zagaya da gwamnan a harabar makarantar, ya ce tun da aka kafa makarantar ba ta taba samun wutar lantarki ba.
Ya kuma koka da rashin isassun kayan aiki kamar asibitin, daki da kuma kayan aikin bita don horar da daliban sana’o’in dogaro da kai.
Bayan kammala duban, Gwamna Dauda ya bayar da umarni ga ma’aikatun da ke da alhakin tabbatar da ganin an gyara makarantar da masallatai da kuma kicin ta cikin yanayi mai kyau don gudanar da aikinta na gyaran yara.