Gamayyar kungiyoyin fararen hula (CLO) ta jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa ayyana sabbin shugabannin tsaro da za su lura da tsaron kasarnan.
Shugaban kungiyoyi na jihar Anambra, Vincent Ezekwueme, shi ne ya jinjinawa Buhari a Inugu.
Ezekwueme ya ce nadin sabbin shugabbanin tsaro an yi shi a kurarren lokaci, amma duk da haka an dauki matakin ya dace. Ya ce kuma hakan ya dace da abin da ‘yan Nijeriya suke son ji dama.
Ya ce bisa hakan suna jinjinawa shugaba Buhari.
A karshe CLO ta yi kira ga sabbin shugabannin tsaron, da za su dauki matakan da suka dace wajen dakile tasirin Boko Haram, ‘yan bindiga da masu garkuwa da jama’a.