Jamhuriyar Nijar dake fuskantar yawaitar hare -haren daga kungiyoyi masu ikirarin jihadi, ta bude makarantar soji ta farko a Yamai babban birnin kasar domin horas da hafsoshinta masu zuwa.
Da yake jawabi yayin bukin kaddamar da makarantar, Shugaba Mohamed Bazoum ya ce kasarsa, a matsayinta na makwabciyar Libya mai fama da tashin hankali, dole ne ta yi aiki kan bukatun tsaro duba da matsayinta a tsakiyar yankin da ke fuskantar ayyukan ta’addanci.
Cibiyar za ta zama “muhimmiyar hanyar ƙarfafa tsaron ƙasar dake da iyakoki da Najeriya da Benin a kudunci, sai Burkina Faso da Mali a yamma, Algeria da Libya a arewaci sai kuma Chadi dake gabashinta.
Rukunin farko zai kunshi jami’ai 26 da aka dauka daga sojoji, jandarma da masu tsaron kasa wadanda za su yi horo na watanni tara a karkashin malamai na kasa, in ji kwamandan makarantar Abdoul Razak Ben Ibrahim.
Shugaban Bazoum ya kara da sanar da kirkirar wata makarantar sojojin sama a Agadez da ke arewacin kasar da kuma cibiyar da za ta koyar da kananan sojoji sabbin dauka a yankin Tahoua dake yammacin kasar da zai iya daukar dalibai dubu biyar a shekara daga shekara mai zuwa.