Rundunar ‘yan sanda a Ogun ta ce wasu ma’aurata, Mba Moses da Florence Moses, sun shiga hannun akan zargin kashe wani Mark Kalu bayan wanda abin ya shafa ya samu rauni a fada a tsakaninsu.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Omolola Odutola ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Abeokuta ranar Asabar.
Karanta nanYanzu-Yanzu: Kayode-Laguda Ya Samu Tikitin Takarar Kujerar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa
Odutola ya bayyana cewa, jami’in ‘yan sanda reshen yankin Odeda na jihar a ranar Asabar da karfe 7:00 na safe ya samu rahoton mutuwar mutumin mai shekaru 45 da haihuwa.
Kakakin ya ce marigayin ya samu raunuka a wani fadan da ya faru a ranar 8 ga Oktoba, 2023, a kasuwar Osiele.
Rikicin ya faru ne a dandalin kasuwa tsakanin marigayi Mark Kalu da wasu ma’aurata, Mba Moses mai shekaru 50 da matarsa, Florence mai shekaru 40, wanda ya kai ga mutuwar Kalu,” inji shi.
Da farko dai Babaloja na Osiele da kuma shugaban al’ummar Igbo ne suka yi kokarin sasantawa tare da samun matsaya mai kyau amma hakan ya ci tura.
Duk da haka, yanzu an tsare wadanda ake zargin domin gudanar da bincike na farko kan lamarin,” in ji ta.
Ta bayyana cewa an ajiye gawar marigayin a dakin ajiyar gawarwaki na Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Idi Aba domin a bincike ta.
A wani labarin kumaAn Bukaci Tinubu Ya Sallami Ma’aikata Masu Digiri Yar Kwatano Daga Aiki
An yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakin kamo wadanda suka mamaye manyan ofisoshin gudanarwa da takardun shaidar karatun jami’a na jabu da sauran su.
Shugaban Hukumar Kare Hakkokin Bil Adama ta Duniya, Ecology and Marine Marine, Afirka, Alhaji Musa Saidu ne ya yi wannan kiran a zantawarsa da jaridar Vanguard.
Inda ya jaddada cewa badakalar takardar shaidar bogi da aka yi a baya-bayan nan da aka alakanta da wata jami’a a jamhuriyar Benin, wata manuniya ce da ke nuna cewa ‘yan Najeriya da dama da ke rike da manyan mukaman gwamnati. masu digiri na jabu na jami’a.