- Masanin harkokin kudi, kuma tsohon ma’aikacin gwamnati, Fuad Kayode-Laguda, ya zama dan takarar jam’iyyar APC a zaben cike gurbi
- Wannan na zuwa ne bayan da INEC ta Sanya Ranar gudanar da Zabukan Cike Gurbi a wasu jihohin Tarayya
- Dan Takarar Majalisar ya lashe zaben ne bayan samun nasara a zaben fidda gwani
Masanin harkokin kudi, kuma tsohon ma’aikacin gwamnati, Fuad Kayode-Laguda, ya zama dan takarar jam’iyyar APC a zaben cike gurbi na majalisar wakilai na mazabar Surulere 1.
Kayode-Laguda ya zama dan takarar ne ta hanyar lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar da aka gudanar ranar Asabar a filin wasa na Teslim Balogun da ke Surulere a Legas.
KARANTA WANNAN: Kisan Filato: Wasu Mata Masu Zanga-Zanga Sun Kone Gidan Wani Basaraken Gargajiya
Zaben fidda gwani da aka shirya gudanarwa a ranar 3 ga watan Fabrairun 2024, na nufin maye gurbin tsohon kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, wanda ya wakilci mazabar kafin shugaba Bola Tinubu ya nada shi a matsayin shugaban ma’aikatan fadar sa.
A wani labarin kuma, Matasa Suna Shan Fitsarin Mutum da Kashin Kadangare – NDLEA
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa matasa a jihar Borno suna shan fitsarin dan adam, wanda aka ajiye har na tsawon kwanaki 10
Wadannan sabbin sinadarai masu tayar da hankali da ake yawan amfani da su suna Matukar barazana ga rayuwa
NDLEA ta kama tan 4.5 na haramtattun kayan maye tare da kama mutane 863 da ake zargi
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta bayyana cewa matasa a jihar Borno suna shan fitsarin dan adam, wanda aka ajiye har na tsawon kwanaki 10, a matsayin madadin muggan Kwayoyi.
Kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar Borno Iliyasu Mani ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri.