Matashi ya yi wa ƴan mata 2 ƴan gida ɗaya fyaɗe a Jigawa
Rundunar ƴansandan jihar Jigawa ta tabbatar da cafke wani ɗan shekara 45 bisa zargin yin fyade ga ƴan mata 2 ƴan gida daya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansandan ASP Zubairu Aminudden Ismail ya shaida wa jaridar Daily Post al’amarin, da ya faru a kauyen Kiyako na karamar hukumar Birnin Kudu a jihar.
Ya shaida cewa wanda ake zargin ya yaudari ƴan matan masu shekaru 12 da 13 ya shiga da su dakinsa inda ya yi masu fyaden.
Majiyar mu ta kuma shaida cafke wani matashin, Abubakar Adamu a kauyen Zanga na karamar hukumar ta Birnin Kudu, wanda shima ake zargi da aikata fyade ga wata yarinya yar shekara 16, kuma bincike na ci gaba da gudana akan lamarin.