An kama tsohon ɗan majalisa da wasu mutum shida kan aikata ta’addanci
Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta ce ta kama wasu mutane bakwai da ake zargi ciki har da wani tsohon kansila da ake zargi da aikata ta’addanci a cikin babban birnin Enugu.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Daniel Ndukwe ya fitar, ya ce ‘yan sandan sun kwato bindigogi shida, harsashi 16 masu rai, da wata mota da aka kwace daga hannun mutane shidan.
KARANTA WANNAN LABARIN:EPL: Merson Ya Yi Hasashen Yadda Wasan Liverpool,Arsenal da Man Utd Zai Kasance
PPRO ya bayyana cewa jami’an ‘yan sandan da ke aiki a sashin ‘yan sanda na Abakpa, tare da hadin gwiwar kungiyar masu lura da unguwanni, a ranar 6 ga watan Disamba, sun kama tsohon dan majalisar, Henry Agbo Ogbonna da wasu shida.
Ya ce tsohon dan majalisar ya wakilci yankin Ikiriki 6 a karamar hukumar Enugu ta Kudu.
“Wadanda ake zargin da ‘yan bindigar da suka tsere, sun kai farmaki kan mutumin da aka kashe, inda suka kwace masa wayoyinsa tare da kwace motarsa kirar Toyota Camry a cikin lamarin,” inji shi.
Ya bayyana cewa suna gab da tserewa ne sai jami’an ‘yan sanda suka far musu, inda suka kama wanda ake zargin, sannan suka kwato bindiga guda daya kirar gida biyu da motar.
A wani labarin kuma:Rundunar Sojin Najeriya ta yiwa manyan sojojin ta karin girma
Majalisar Sojojin Najeriya ta amince da karin girma ga Birgediya-Janar 47 zuwa Manjo Janar, yayin da Kanar 75 kuma aka daukaka su zuwa matsayin Birgediya Janar.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana sunayen wadanda aka kara wa matsayin Manjo Janar da suka hada da: Birgediya Janar WB Etuk, Kwamandan Kwalejin Dabaru da Gudanarwa na Sojojin Najeriya, Birgediya Janar JE Osifo, Kwamanda a Makarantar Kudi da Gudanarwa ta Sojojin Najeriya.