- An kama wani Insifektan ‘Yan sanda na bogi a jahar Legas.
- Yana yawo a babur ɗinsa yana karɓar kuɗi a wajen mutane.
- Tuni rundunar ‘yan sandan jahar ta Legas tayi ram da shi.
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke ɗan sandan bogi da yake bayyana kansa a matsayin Insifektan ‘yan sanda a karkashin rundunar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar wa manema labarai kamun a ranar Talata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bai Halatta Ga Mutum Ya Auri Mace ‘Yar soshiyal midiya ba.
Hundeyin ya ce wanda ake zargin ya daɗe yana aiki da babur ɗinsa mara rajista domin gudanar da zirga-zirgarsa ta kasuwancin a unguwar Ikorodu da ke jahar Legas
Ya ce tawagar ‘yan sandan sintiri da ta yi zargin jami’in na ƙarya ne ta kama shi domin yi masa tambayoyi a ranar Lahadi da misalin karfe 10:22 na dare.
Yace; “Wanda ake zargin ya yi kama da jami’i kuma ya yi ikirarin cewa shi Insifekta ne na ‘yan sanda.
Wanda ake zargin ba shi da takamaiman bayanan ‘yan sanda kuma katin shaidar da aka samu a wurinsa ba na gaskiya ba ne.
“Wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda kuma an kama babur ɗinsa.
“Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu kan yin sojan gona nan ba da jimawa ba,” in ji Hundeyin.
Kotu Ta Yi Hukuncin Kisa Ga Mutane Uku Saboda Satar Cajar Waya
A WANI LABARIN KUMA: Wata babbar kotu da ke jihar Ekiti a kuma birnin Ado Ekiti ta yanke wa wasu mutane uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun su da laifin hada baki da kuma fashi da makami.
Wadanda aka yankewa hukuncin sun haɗa da Omotayo Deji da Chidiebere Ifeanyin da kuma Bolaji Usman.
An gurfanar da su ne a gaban kotun a hannun mai shari’a Bamidele Omotoso a ranar 21 ga watan Janairun 2020, bisa tuhume tuhume guda huɗu.