An kama wani mutum da laifin sayar da hotuna da bidiyon tsiraicin wata budurwa
An kama wani mutum mai suna Chinedu Ezeudu dan asalin kauyen Ndi Ikpa Ezinato da ke karamar hukumar Awka ta Kudu a jihar Anambra da laifin sayar da hotuna da bidiyon wata mata tsirara a shafukan sada zumunta.
An dai zargi mutumin da fallasa waɗannan hotuna da bidiyon ne bayan yunkurin neman kudi daga hannunta ya ci tura.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gidaje 1,000: Babu Wanda Ya Isa Ya Ajiye Fulani A Jaharmu-Mazauna Benue
Ana zargin mutumin ya sayar da bidiyon tsiraicin budurwar ga mutanen da suka bukaci hakan akan Naira dubu 3,000.
Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta cafke wanda ake zargin bayan itama mai hotunan ta kai rahoto ga ofishin kwamishiniyar harkokin mata da walwalar yara, Misis Ify Obinabo.
Mai taimaka wa kwamishinan yada labarai, Miss Chidinma Ikeanyionwu ta ce: “wadda aka saida hotunan ta na tsiraici ta ce ta rasa memorin wayar ta a watan Maris, 2023, amma daga baya wanda ake zargin ya tattauna da ita a watan Yuni, tare da neman makudan kudade domin kada ya fallasa bidiyoyin tsirara.
“Lokacin da ta ki biyan kudin, wanda ake zargin ya yi barazanar sanya bidiyon a dukkanin shafukan sada zumunta.
Ta ce wanda ake zargin ya ci gaba da fitar da bidiyon a Facebook, Whatsapp da sauran kafafen sada zumunta, ciki har da sayar da su ga wadanda suka nema.
Ikeanyionwu ya ce: “Lokacin da wadda ta kai ƙara tare da rakiyar Honarabul Ejike Okechukwu ta kai rahoto ofishin kwamishinan mata da walwalar jama’a na jihar Anambra, rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta yi gaggawar cafke wanda ake zargin.”
Ta ce wanda ake zargin wanda a halin yanzu yana hannun ‘yan sanda za a gurfanar da shi a gaban kotun hukunta laifukan yara da jima’i da jinsi da ke Awka da zarar an kammala bincike.
A wani labarin kuma:Tinubu Ya Gaji Ayyukan Tituna Na Naira Tiriliyan 14 daga Gwamnatin Buhari – Minista
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da yunkurin jigilar buhu goma sha shida na tabar wiwi ta Indiya zuwa kauyen Ndayako da ke karamar hukumar Mokwa a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PRO), DSP Wasiu Abiodun, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Minna, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar 6 ga watan Satumba, 2023, bisa ga sahihan bayanan da jami’an ‘yan sandan da ke aiki a sashin Mokwa suka samu. .