An kama wani Mutum kan zargin kashe Ƙananan Yara
Rundunar Ƴan sandan jihar Adamawa ta cafke wani mutum mai suna Barnabas Abduneza mai shekaru 40 bisa zargin kashe karamar yarinya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mawaki Davido Zai Angwance Da Chioma A 2023
Wani mazaunin kauyen Kpasham da ke karamar hukumar Demsa a jihar Adamawa, Abduneza, ya kai wa mamacin da mahaifiyarta hari a makon jiya, 29 ga watan Satumba a kauyen Kadamti, lamarin da ya yi sanadin mutuwar karamar yarinya da kuma mummunar rauni a jikin mahaifiyar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Sulaiman Nguroje, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya samu da safiyar Asabar, ya ce, “Bayan harin da aka kai wa wata mata da yaronta a kauyen Kadamti da ke karamar hukumar Numan a ranar 29/9/2022 da wanda ya yi sanadiyar mutuwar jaririn tare da raunata mahaifiyar, jami’an rundunar ‘yan sandan da ke yankin Numan Dibision, Ma’aikatan Operation Farauta da wasu mutane nagari suka fantsama tare da kama wani dangane da laifin.
“Wanda ake zargin, Barnabas Abduneza mai shekaru 40, mazaunin kauyen Kpasham, a karamar hukumar Demsa, an kama shi ne bayan wani sahihan bayanai.”
A cewarsa, ‘yan sandan sun kwato Takunkumin fuska da wasu baka da kibau, da kuma wasu muggan makamai daga hannun wanda ake zargin.
A wani labarin kuma: Deji Adeyanju ya shawarci ASUU kan Matakin da ya kamata ta ɗauka akan Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara
Wani mai fafutuka, Deji Adeyanju ya shawarci kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) kan abin da za ta yi game da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke ranar Juma’a na neman malaman da su koma bakin aiki cikin gaggawa.
Adeyanju, a wani sako da ya wallafa a ranar Asabar, ya bukaci kungiyar ASUU da ta janye yajin aikin da ta kwashe watanni bakwai tana yi domin yin biyayya ga hukuncin da kotu ta yanke.