Wakilinmu Ahamed Musa Gumel
Jirgin karshe mai dauke da maniyata 343 ya bar filin jirgin saman Dutse da misalin karfe 6.47 na safiyar asabar din nan da ta gabata.
Daraktan aiyuka na hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa Alhaji Ahmad Umar Labbo, yace maniyatan sun kunshi na kananan hukumomin Roni, Yankwashi, Malam-Madori, Kaugama , Hadejia, Birniwa,Guri, Kirikasamma , Kazaure da kuma wadanda suka biya ta hedikwatar hukumar.
Jirgin na karshe ya kunshi sakataren zartarwa na hukumar Alhaji Muhammad Sani Alhassan, da sauran daraktocin hukumar
Sai dai kuma a wannan shekara babu Amirul Hajj da kuma tawagar gwamnatin jiha a aikin hajjin bana, ko me yasa haka?
Idan za a iya tunawa jirgin farko na maniyatan Jigawa ya bar kasar nan zuwa kasa mai tsarki a ranar larabar data gabata dauke da maniyata 555 da suka fito daga kananan hukumomin Sule tankarkar, da Garki, da Gagarawa, da Gumel, da Taura, da Ringim, da Maigatari, da Babura, da Dutse, da Kiyawa, da Jahun, da Miga, da Gwaram, da Buji, da Birnin Kudu, da Kafin Hausa, da Auyo, da kuma Gwiwa.