Kamfanin gine-gine naTEC Ltd. ya ce gadar sama ta Kofar Mata da kudinta ya kai Naira biliyan 15 mai sunan shugaban darikar Qadriyya, Sheikh Qaribullahi Nasiru Kabara ya kusan kammala domin an yi kashi 90%.
Manajan aikin, Engr. Steven Steven ya bayyana hakan ne a cikin makon nan a zantawar da yayi da manema labarai kan yanayin aikin.
Jaridar Dimukuradiyya ta ruwaito cewa gadar sama mai nisan kilomita 2.5 da ta taso daga Kofar Mata, ta bi ta Kantin kasuwar Kwari, Ibrahim Taiwo Road, Singer Market da kuma hade da gadar sama ta Murtala Mohammed, an bayar da ita ne a shekarar 2018.
Steven ya ce, gadar sama mai dauke da sanduna 1 a mahadar IBB da mahadar titin Ibrahim Taiwo ya cika duk wata ka’ida ta kasa da kasa domin ana bayar da iko gainjiniyoyin da suka dace daidai da ingantattun ayyuka.
Engr. Steven ya ce dole ne a ruguje gine-ginen da ke kusa da gadar ta yadda za a samar da isasshen sarari don zirga-zirgar ababen hawa. “ ginin da ke kusa da gadar dole ne a ruguje su don kare lafiya da samar da karin sarari don zirga-zirgar ababen hawa. Mun tattauna da gwamnati da ma’aikatar ayyuka kuma hakan zai faru ne bayan an biya diyya ga wanda da abun ya shafa’’.
Manajan aikin ya yabawa gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar da take baiwa kamfanin wajen raba kudade da sauran tallafi. ”Hakazalika, dole ne mu yaba wa mutanen saboda hadin kai da fahimtar da suke yi da ginin da ake gudanarwa,” in ji Steven.