Kasa da sa’o’i 24 da kashe mutum 11 a Kurmin Masara da ke masarautar Atyap na karamar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a Atisa da ke Kurmin Masara, inda suka kashe mutum biyar a daren Litinin.
Wata majiya daga wani kauye da ke makwabtaka da ita da ta tabbatar wa wakilinmu harin ta ce ‘yan bindigar sun isa wurin ne da misalin karfe 9:50 na dare inda suka yi awon gaba da wasu mutane, bayan sun kwashe tsawon sa’a guda a yankin.
“Saboda yawancin mazauna garin sun bar gidajensu a Kurmin Masara, maharan sun yanke shawarar kai farmaki kan Atisa, wani matsugunin da ke kusa da Kurmin Masara.”
Shugaban matasan masarautar Atyap, Jibrilu Joseph, ya yi gargadin cewa barayin na da manufar shafe su ne Baki daya daga doran kasa
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta dauki kwararan matakai domin kare Al’umar yankin da ma dukiyoyin su.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, shugaban karamar hukumar Zangon Kataf, Francis Sani, ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an samu zaman lafiya, kuma masu aikata laifin sai an binciko su.