Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya ce an kashe zunzurutun kudi Naira biliyan 12 wajen sayen motocin kashe gobara guda 10 a filayen jiragen saman Najeriya.
Sirika ya bayyana hakanne a ranar Lahadi 2 ga watan Afrilu cewa ya kaddamar da motocin kashe gobara guda goma ga hukumar kula da filayen jiragen sama ta tarayya, FAAN.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Kame Wasu Mutane Biyu da Ake Zargi Da Hallaka Wani Jami’in Tsaro
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Sirika ya bayyana cewa FAAN ba ta sayi motocin kashe gobara ba cikin shekaru 15.
Ya wallafa a shafinsa na twitter cewa: “Kawai ya kaddamar da manyan motocin kashe gobara guda 10,kan jimlar kudin sama da Naira biliyan 12.”
“Tsaro shi ne abinda Buhari ya mayar da hankali a kan harkokin sufurin jiragen sama, tun shekarar 2015. Har zuwa yanzu FAAN ba ta sayi sabbin manyan motoci ba a cikin shekaru 15.”
A wani labarin kuma, SDP Ta Dakatar da Dan Takararta Na Gwamna Da Wani Jigon Jam’iyyar
Jam’iyyar SDP a jihar Oyo ta dakatar da dan takararta na gwamna a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, Michael Lana, da sakataren jam’iyyar Idowu Owokoya, bisa zarge-zargen cin amanar jam’iyyar.
Dakatarwar tasu ta na kushe ne ta cikin wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar SDP na jihar Oyo, Michael Okunlade, kuma aka aika zuwa hedikwatar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja ranar Juma’a.