An rantsar da Firaministan Habasha-Ehiopia Abiy Ahmed a ranar Litinin domin jagorantar ƙasar ya zuwa shekaru biyar, a dai-dai lokacin da gwamnatin sa ke fuskantar matsaloli da dama, da suka haɗa da rikicin watanni na Arewacin yankin Tigray.
Abiy wanda ya lashe zaben Firaminista a watan yuni, ya karɓi rantsuwar kama aiki, daga Babban Jojin Kotun ƙoli na ƙasar, Mai Shari’a Meaza Ashenafi, biyo bayan rantsar da shugaban majalisa da mataimakin sa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fitaccen Masanin Kimiyyar Siyasa, Farfesa Yahaya, Ya Rasu
“Ni Abiy Ahmed Ali, yau a majalisar dokoki ta ƙasa, na karɓi kujerar Firaminista, a yayinda nayi alƙawarin daukar duk nauye-nauyen ƙasa, tare da aiki da kundin tsarin mulki da aka ɗora mani,” ya faɗi haka a lokacin da Babban Jojin Ƙasar, Mai Shari’a Meaza Ashenafi yake rantsar dashi.
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na ɗaya daga cikin Manyan Baƙi daga ƙasashen ƙetare da suka halarci rantsuwar, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar ta ruwaita.