By Ishaq Dabai
Jam’iyyar (APC) reshen jihar Katsina ta yi nasarar rantsar da wakilan zartarwa 36 da aka zaba ta hanyar yarjejeniya.
An rantsar da Alhaji Sani Ahmed a matsayin shugaba, Bala Abu Musawa a matsayin mataimakin shugaba, Shitu Shitu, tsohon shugaban jam’iyyar na jihar a matsayin sakatare da Babangida Aliyu a matsayin ma’aji.
Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Ahmed El Marzuk ne ya rantsar da shugabannin jam’iyyar a filin wasa na Muhammadu Dikko dake Katsina.
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina yayin da yake jawabi a wurin taron ya yabawa dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar kan goyon bayan da suka nuna, fahimta da hakuri kan yadda ake gudanar da babban taron a matakin mazabu, kananan hukumomi da jihohi.
Masari ya yi kira ga membobin jam’iyyar da su baiwa sabbin zababbun shuwagabannin goyon bayan da suka cancanta don ba su damar jagorantar jam’iyyar zuwa babban zaben na shekarar 2023 yayin da ya umarce su dasu kasance masu hadin kai.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Gwamnan ya kuma yabawa ‘yan takarar da suka janye daga takarar don ba da damar karba ta hanyar yarjejeniya kamar yadda masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka amince da farko.
A nasa jawabin, Alhaji Aliyu Kumo, shugaban kwamitin majalisar jiha daga hedikwatar APC ta ƙasa ya gabatar da rahoton taron na jihar ga gwamna Masari.