Hukumar kiyaye haddura FRSC ta kasa shiyar jihar Kano ta ce, za a kulle gadar Tsamiya Bakin na wucin gadi da a yau Litinin.
Kadar dai da ta hada garin da Kwana Huguma-Kari dake iyakar jihar Kano da kuma Jigawa.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamandan hukumar shiyar jihar Mr Zubairu Mato ya fitar yau litinin a garin Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: ASUU ta yi barazanar sake shiga yajin aiki
Jaridar NAN ta ruwaito cewa, Kadar da tahada garin Tsamiya Bakin Gada a jihar Kano, zuwa Huguma -Kari ta lalace ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da akasa a Yan kwanakin nan.
Mato ya ce, ” lalacewar gadar ya kasan ce babban barazana ga masu amfani da abbaben hawa a yankin.” Inji shi.
” Za a rufe gadar daga ranar 30 ga Agusta shekarar 2021, Kuma za’a sauya hanyar zirga-zirgar zuwa wata hanyar ta daban a jihar Jigawa, kamar wacce take Birnin Kudu na matattarar motoci na kusa da Kwalejin horas da Unguwar zoma na garin Kengere, kafin Ma’aikatar aiyuka ta kasa, ta gyara gadar”
“Saboda haka, hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC na sanar da al’uma musamman wadanda ke amfani ababen hawa, da su kaurace wa hanyar saboda yuwuwar zaftarewar gadar.”