By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan sandan tafi da gidanka a yankin Tike dake karamar hukumar Mayo Belwa a jihar Adamawa.
Wani mazaunin garin yace dan sandan da aka sace an yi kuskuren cewa wani attajiri ne, wanda yasa masu garkuwar suka yi awon gaba da shi.
Wanda lamarin ya shafa yana daya daga cikin jami’an tsaro wadanda aka tura yankin don magance matsalar garkuwa da mutane, wanda ya zama ruwan dare a yankin.
A cewar wata majiya, ‘yan bindigar sun kai farmaki ne a kan babura da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Asabar, inda suke neman wani attajiri mai suna Idi Bage.
“Mutumin da ‘yan bindigar ke nema ya mallaki wani katafaren gida daura da babbar hanyar Mayo Belwa zuwa Jalingo. Bage mutum ne da aka san shi da ƙawa kamar yadda koyaushe yake sa tufafi mash tsada amma a wannan rana sai yasa marar kyau.
“An yi sa’a a gare shi, bai yi ado da kyau ba a wannan rana, wanda kaddara Abin takaici, ta fada kan MOPOL da ke sanye da riga mai tsadar gaske a wajen bikin Kirsimeti, an yi kuskure da attajirin,” inji majiyar.
Operation Farauta ya kunshi sojoji da ‘yan sanda da mafarauta. An kafa ta ne domin magance ayyukan ‘ya’yan Shila da masu garkuwa da mutane a Jihar Adamawa.
Mayo Belwa da makwaftan kananan hukumomin sun shaida ayyukan masu garkuwa da mutane da dama a yankin.
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje, ya ci tura domin bai dauki waya ba.