By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni daga jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya, sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun sake yin garkuwa da mata sama da 20 sakamakon hare-haren da aka kai wasu kauyuka 15 dake unguwar Gusau, babban birnin jihar.
A rahoton da BBC Hausa ta fitar, wasu mazauna kauyukan Geba da Gidan Kaura, da wasu mazauna kauyukan karamar hukumar Gusau, sun shaida wa BBC cewa ‘yan fashin sun mamaye yankunansu, sun kashe mazaje tare da lalata dukiyoyinsu.
’Yan bindigar dai sun yi garkuwa da mata da ‘yan mata, suka tafi da su,” inji su.
Daya daga cikin mazauna yankin ya ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mata 10 a Kura, a Bayauri, sun yi garkuwa da 9. Sun kuma shiga wani kauye mai suna Gana suka yi awon gaba da 7 kafin su wuce Duma, suka kuma yi garkuwa da wasu matan 7, duk hakan ya faru ne kafin safiyar ranar Lahadi.
Rahotanni sun bayyana cewa, kauyuka da dama sun zama ba kowa, a sakamakon mutanen kauyen sun yi kaura zuwa babban birnin jihar, Gusau.
Wani dan unguwar dake yin hijira zuwa Gusau, ya ce yanzu haka sun gudu zuwa al’ummar Damba da ke cikin babban birnin jihar Zamfara, Gusau.
“Muna da mata da yara da masu ciki, babu abinci. Idan ka ga inda suke kwana cikin wannan sanyi, kamar babu gwamnati,” wani mazaunin garin Damba ya yi wannan zargin.
Kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, ya tabbatar da cewa an kai harin ne a Geba.
Sannan yace, “Akwai sojoji da ke aiki a yankin, sun je Geba, sun gamu da mutane 3 da suka jikkata, sojojin sun tarwatsa ‘yan fashin.”
Kwamishinan ya kara da cewa ba gaskiya ba ne cewa sama da kauyukan da aka kai hari, jami’an tsaro basu kai ziyara wajen aikin ceto ba.
Hare-haren na Zamfara ya zo ne a daidai lokacin da hukumomi suka bayyana cewa jami’an tsaro sun kama wasu ‘yan bindiga da aka tarwatsa a maboyarsu tun da farko, wadanda suka je wani asibiti domin yi musu magani.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Tsawon wasu shekaru, Zamfara na cikin jihohin Arewa da ke fama da matsalar ‘yan fashi, lamarin da ya kai ga daukar hankali a jihohin Sokoto, Katsina, Kaduna da makwabta.
A makon da ya gabata, ‘yan bindigar sun kona fasinjoji sama da 20 a cikin wata mota a Sokoto, lamarin da ya jawo cece-ku-ce da kuma fusata a tsakanin wasu ‘yan Najeriya da ke zargin gwamnati na barin ‘yan fashin su yi abinda suke si, ba tare da kalubalantarsu ba.