Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da cewa an sako daya daga cikin shugabanninta na sa ido, wanda aka yi garkuwa da shi a jajibirin zaben gwamna a jihar Bayelsa.
Wanda aka yi garkuwa da shi a jirgin ruwan Amassoma da ke karamar hukumar Ijaw ta kudu, ya samu ‘yancinsa ne a ranar Asabar.
Karanta nanZaben Imo: Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Koka Kan Sayen Kuri’u, Da Sauran Munanan Ayyuka
Shugaban sashen wayar da kan masu kada kuri’a na INEC a jihar Bayelsa, Wilfred Ifogah ya tabbatar da hakan.
A cikin sanarwar a hukumance, Ifogah ya ce hukumar zabe mai zaman kanta, ofishin jihar Bayelsa, na farin cikin sanar da masu ruwa da tsaki da ‘yan kasar da abin ya shafa a Najeriya cewa an sako jami’in hukumar INEC SPO da aka yi garkuwa da shi a jajibirin zaben kuma yana nan cikin koshin lafiya.
A baya dai INEC ta bayar da rahoton sace daya daga cikin shugabanninta na sa ido a jihar Bayelsa a jajibirin zaben. An tura jami’in ne a yankin Registration Area 06 (Ossiama) a karamar hukumar Sagbama kuma an yi garkuwa da shi ne a lokacin da yake jiran ya hau jirgi a jirgin Amassoma.
A wani labarin kumaDino Melaye Ya Bukaci Hukumar INEC Ta Soke Zaben Kananan Hukumomi Biyar
Zuwa yanzu dai zaben jahar ta Bayelsa na kara zafi a tsakanin gwamna mai ci Douye Diri da kuma dan takarar gwamnan jahar a karkashin jam’iyar APC kuma tsohon gwamnan Jahar Thymipre Sylva.
Sylva wanda tsohon ministan Neja Delta ne a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga zaben ne duk da korafe korafe da aka samu akan rashin cancantar shigarsa zaben,bayan ya mulki jahar mai arzikin man fetur tsawon shekaru 5.